Hukumar kiyaye hadurra ta kasa (FRSC) reshen jihar Bauchi, ta ce ta tura jami’ai 1,060 domin tabbatar da bukukuwan Kirsimeti da na sabuwar shekara ba tare da hadari ba a jihar.
Kwamandan sashin, Mista Yusuf Abdullahi, ya shaida wa Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya NAN a ranar Litinin a Bauchi, cewa za a kuma tura motocin sintiri 12 da motocin daukar marasa lafiya guda shida domin kara kai daukin gaggawa a cikin wannan lokaci.
Abdullahi ya kara da cewa, an samar da kayan aiki ne ga wasu jami’an hukumar 730, da jami’ai na musamman guda 300, da ma’aikatan lafiya 30.
Kwamandan sashin ya ce ana sa ran za su hada dukkan masu ruwa da tsaki a yankunan domin tabbatar da samun nasarar akare afkuwar hadurran ababen hawa a lokutan bukukuwa da ma bayan hakan.
“Rundunar ta kammala shirye-shiryen tabbatar da Kawo dauki yayin da aka samu hadurran ababen hawa, a lokutan bukukuwan Kirsimeti da na sabuwar shekara.
“Haɗin gwiwa mai inganci da hukumar kula da tituna ta tarayya (FERMA) zai yi matuƙar mahimmanci wajen gyara wasu ɓangarori na titunan da kuma kawar da cikas.
“Za a kawar da kasuwanni daga manyan tituna ta hanyar amfani da hadin gwiwar hukumar haraji,” in ji shi, ya kara da cewa jami’an FRSC za su tabbatar da zirga-zirgar ababen hawa a fadin jihar.