Ranar Lahadi ministan harkokin cikin gida na Jamus, Horst Seehofer ya goyi bayan a ci gaba da gasar Bundesliga ta kakar 2019-20 ba tare da ‘yan kallo ba.
A makon da za mu shiga, gwamnatin Jamus za ta yi taro tare da kungiyoyi da masu ruwa da tsaki kan zakulo hanyoyin da ya kamata a bi domin karkare gasar shekarar nan.
Kodayake tuni wasu kungiyoyin Jamus suka koma atisaye na daidaiku da na rukuni-rukuni saboda bin dokar da gwamnati ta saka ta bayar da tazara kamar yadda rahoton Bbc ya tabbatar.