Shugaban Kwamitin Ruƙon Jam’iyyar APC na Ƙasa Mai Mala Buni ya ziyarci jigon jam’iyyar na ƙasa Bola Tinubu a Lagos.
Buni, Wanda shine Gwamnan Jahar Yobe, yabi sahun sama da mutane 30 da suka ziyarci jigon jam’iyyar a watannin baya, musamman a lokacin tafiyar sa ta neman lafiya zuwa Landan.
KARANTA WANNAN LABARIN: KAN ZARGIN LALATA DA ƊALIBAI: Kwalejin Tarayya A Bauchi Ta Kori Malamai
A cikin wani rubutu da aka wallafa a shafin Facebook, an hangi Bola Tinubu da Gwamnan Jahar Yobe a tare.
Haka zalika, hoton anyi mashi rubutu da #asiwaju4president2023,
A wani Labarin kuma
Wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su waye ba sun kai hari tare da kashe mutane biyu a kauyen Ungwan Taila, da ke karamar hukumar Zangon Kataf a jihar Kaduna.
Sojojin Operation Safe Haven ne suka ruwaito wannan labarin.
Kwamishinan tsaro da kula da harkokin cikin gida na jihar Mista Samuel Aruwan ne wanda ya tabbatar da hakan, a cikin wata sanarwa da ya fitar, inda ya ce, sojojin sun isa kauyen ne bayan sun gano cewa, maharan sun kashe mazauna garin guda biyu.
A cewar sanarwar, Gwamna Nasir el-Rufai ya bayyana matukar damuwar sa kan harin da yayi sanadiyar asarar rayuka a yankin.
A karshe Gwamnan ya yi addu’ar Allah ya jikan mamatan, sannan ya mika ta’aziyyar sa ga iyalan su.