Tsohon Mataimkain shugaban Kasa Atiku Abubakar ya ce sun bada gudunmawa matuka wajen bunaksa harkokin dimokuradiyya a kasar nan shi da Shugaban Jam’iyyar APC Bola Ahmad Tinubu.
Wannan jawabi na zuwa ne a shafin Tuwita na Alhaji Atiku Abubakar yayin da ke taya Tinubu murnar cika shekara sittin da tara da haihuwa.
Ya rubuta cewa “Mun sha gwagwarmaya matuka ni da Tinubu wajen bunkkasa Dimokuradiyya a kasar nan”.
“A yayin da kake murnar ranar haihuwar ka, Ina rokon Allah da Ya baka tsawaita maka kwana don ci gaba da gwagrmaya da ka saba ta hanyar kyakkayawar shugabanci, ina taya ka murna Abokina kuma dan uwa na” in ji Atiku.