Daga Inuwa Hamisu
Gwamnan Kaduna, Malam Nasir Ahmad El Rufa’i wanda a iya cewa ya shahara wajen samar da ayyukan cigaban Jihar sa ta Kaduna, ya sami Nasarar murkushe jam’iyar Adawa ta PDP musamman idan akayi duba da Rahotonni dake fitowa daga jihar a halin Yanzu.
Gudunmawar da ya bayar bangaren ababan more rayuwa
Malam El Rufa’i ya Gina gadoji tare da Samar da ingantaccen tsarin harkokin kiwon Lafiya mai dorewa, Har ila yau Malam Nasir Ahmad El Rufa’i ya gina hanyoyin sufuri ciki da wajen jihar da kuma bunkasa harkar Ilmi.
Gwamnan ya kuma samar da doka tare da samar da malamai masu Ilmi domin koyar da ‘ya ‘yan talakawan jihar ta Kaduna.
Sanata Uba Sani Mai wakiltar Kaduna ta tsakiya a majalisar Dattawan Najeriya, ya taka rawar gani, domin Samar da cigaba a Jihar Kaduna Karkashin Gwamnatin Malam Nasir El Rufa’i.
Sanatan Uba Sani ya shahara a majalisar musamman wajen shigar da kudurai masu mahimmanci da suka hada da inganta rayuwar talakawan Jihar.
Sanata Uba Sani ya Samar da jari kala kala ga dumbin Al’ummar jihar kaduna a matsayin sa na Shugaban Kwamitin bankunan Inshora, ya taimaka wajen Samar da kudaden lamuni ga gwamnatin jihar duk domin Samar da ci gaba a Faɗin Jihar.
Samar da ire iren wannan ayyuka yasa Al’ummar jihar kaduna suke goyon bayan Gwamnatin Malam Nasir El Rufa’i.
Ana kallon Sanata Uba Sani a matsayin wanda zai lashe zaben gwamnan jihar Kaduna ba tare da wata Adawa mai karfi ba, idan aka kwatanta da babbar jam’iyar Adawa ta PDP.