Daga wakilin Dimukaradiyya Mukhtar Yakubu Kano
Duk da cewar an dade ba a ganin jaruma Maryann Booth a cikin harkar fim Amma dai ta bayyana irin burukan da take da su a nan gaba a lokacin tattaunawar su da Wakilin Jaridar Dimukaradiyya inda take cewa.
“Burina gaskiya ba karami ba ne, saboda a yanzu da aka daina gani na a fim akwai wajen gyaran gashi da na bude da kayayyaki irin na Mata da Kuma cin abunci a Kano, idan ya bunkasa Ina son ya zama na samar da shi a wasauran manyan garuruwa.”
Ta Kara da cewar “Kuma Ina son na yi furodusin da Kuma Daraktin, su ne babban Burina, domin ban fiye damuwa da aktin ba, saboda idan na yi aure ba zan yi ba. Amma Furodusin da Kuma Daraktin zan iya yin Sa’a, duk da dai shi aure nufi ne na Allah, sai ka ga ka dauki lokaci ka na tsarawa, Amma idan lokaci ya zo shi Kenan. Don haka duk lokacin da na samu dama zan yi aure. Ina fatan dai Allah ya ba ni miji nagari. “