Gwamnatin Birtaniya ta wallafa jerin sunayen ‘yan Najeriya 56 da suka mutu suka bar dukiya mai tarin yawa a kasar Amma ba tare da an gano makusanta da za su gaji wannan dukiyar ba.
Jaridar BusinessDay da ake wallafawa a kasar, ta ce daga cikin dukiyoyin da mutanen suka mutu suka bari har da gidaje, wadanda a karkashin dokokin Birtaniya, matukar aka share tsawon shekaru 30 daga ranar da mai ita ya mutu amma ba a gano magadan mamancinsa ba, dukiyar za ta zama mallakin baitil-mali.
KARANTA ANAN: Zamu Ci Gaba Da Musuluntar Da Maguzawa, Da Koyar Da Ilimin Addini/Zamani – Ganduje
Jaridar Dimokuraɗiyya ta rawaito cewa Gwamnatin Birtaniya ta bayyana sunayen wasu daga mutanen da suka mutu, ciki har da wani mai suna Mark N’woko da ya rasu tun ranar 9 ga watan disambar 1992 a garin Surrey da ke Birtaniya.
Hakazalika akwai wani mai suan Victor Adedapo Olufemi Fani-Kayode, wanda ya mutu ranar 15 ga watan agustan 2001 a Biermingham, to amma har yanzu ba wanda ya gabatar da kansa a matsayin dan uwa ko makusanci domin ya gaje shi.
A wani labarin kuma: An Samu Sauƙin Kiran Waya Don Karbar Kudin Fansa – Pantami
Ministan Sadarwa da Tattalin Arziki na zamani, Farfesa Isa Pantami, ya bayyana cewa duk da cewa masu garkuwa da mutane da ‘yan ta’adda na ci gaba da tattaunawa don neman kudin fansa ta hanyar amfani da wayar tarho, an samu gagarumar nasara tun lokacin da aka fara hada layikan waya da lambar dan kasa ta NIN.
Ministan wanda ya bayyana hakan a garin Umuahia na jihar Abia yayin bikin ranar tantancewa ta duniya, ya ce tun da aka fara kokarin aiwatar da wannan tsari an samu raguwar kiran da ‘yan damfara ke yi wa masu amfani da wayar da ba su ji ba gani.