Kasar Biritaniya za ta bukaci duk matafiya masu shigowa kasar su yi gwajin cutar Covid-19 kafin isowarsu kasar, yayin da kuma masu zuwa daga Najeriya za’a kebe su a otal-Otal dake Kasar don rage yaduwar cutar dau’in Omicron, in ji Ministan Lafiya Sajid Javid a ranar Asabar.
Firayim Minista Boris Johnson ya ce hane-hane tafiye-tafiye ya zama dole don sassauta yaduwar Omicron yayin da masana kimiyya ke ci gaba da aiki don samun cikakken fahimta game da yaduwa da tasirin rigakafin Corona ga nau’in Omicron.
Hukumar Kula da Lafiya ta Burtaniya (UKHSA) ta ce adadin wadanda aka tabbatar sun kamu da cutar Corona samfarin Omicron ya kai 160.
“Mun Sami Wandanan bayanan ne a cikin makon da ya gabata ko makamancin haka, tun lokacin da muka sami labarin Omicron, kuma muna ganin karuwar adadin wadanda suka kamu da nau’in na da alaka da balaguro,” in ji Javid a cikin wani shirin Talbijin na kasar.
Za a sake duba Sabbin dokokin da Burtaniya ta Sanya a kasar ne, a Ranar 20 ga Disamba shekarar nan.
Yayin da Dokar da kasar ta kakaba kan wasu jerin kasashen akan balaguro zai shafi Nigeria ne da musalin karfe 0400 agogon GMT a ranar Litinin.
Ma’aikatar lafiya ta kasar ta ce akasarin wadanda suka kamu da cutar a Biritaniya suna da alakar tafiye-tafiye zuwa kasashen waje daga Najeriya da Afirka ta Kudu.
An saka Afirka ta Kudu da wasu ƙasashe tara na Kudancin Afirka cikin jerin kasashen, a ƙarshen makon da ya gabata, ma’ana ana ba da izinin shiga ne kawai ga Yan ƙasar Burtaniya ko mazauna waɗanda sannan dole ne, su killace kansu a otal.