Shugaban Hafsan Sojojin Nijeriya, Laftanar Janar Tukur Buratai ya kaddamar da gadar da ta karye a watanni baya na Jami’ar Abubakar Tafawa Balewa dake Bauchi. Burutai ya kaddamar da gadar ne bayan da rundunar sojin ta gyara ta.
Har wala yau Burutai ya kaddamar da makarantar Sojoji ta kula da manyan makamai a Bauchi.
Gadar ta Jami’ar ATBU gada ce da ta hada dakunan karatun daliban jami’ar da wuraren karatu, inda a ranar 5 ga watan Agusta gadar ta karye da dalibai a kai wanda ya yi sanadiyyar kashe dalibai uku da jikkata da dama.
Sannan har wala yau Burutai ya kaddamar da jerin dakuna 10 a wurin da aka yiwa suna da ‘Lt.-Gen. Tukur Yusuf Buratai Village’ dake cikin makarantar sojoji masu kula da makami ta Barikin Obienu dake
Manjo Janar James Komolafe, wanda yake shi ne Kwamandan Barikin, shi ne ya wakilci Burutai, inda ya ce gyaran gadar da sojojin suka yi, yana daya daga cikin ayyukan da sojojin ke yiwa fararen hula domin ci gaba da samun hadin kan fararen hula makwabta Barikin.
Ya ce sojoji suna matukar tallafawa bangaren ilimi, walwalar al’umma da kuma samar da tsaro ga al’ummar dake kusa da su.