Daga: Abbas Yakubu Yaura
Shugaban kungiyar Kiristocin Najeriya CAN reshen jihar Neja, Most Rabaran Bulus Dauwa Yohanna, ya yaba da korar wasu jami’an sojoji biyu da hukumar ta yi bisa zargin kashe wani malamin addinin Islama, Sheik Goni Aisami.
Sojojin biyu, kofur Lance John Gabriel da kofur Lance Adamu Gideon,wadanda aka same su da laifi, Rahotanni sun ce Gideon ne ya taimaka wa Gabriel, a lokacin da yake yunkurin sace motar Shehin Malamin na Yobe bayan ya hallaka shi.
KARANTA WANNAN LABARIN: Gwamnatin Tarayya Ta Kaddamar Da Sake Gyaran Babbar Hanyar Gombe Zuwa Yola
Dukkan mutanen biyu sun yi aiki a bataliya ta 241 ta Sojoji har zuwa lokacin da aka kore su a Nguru dake jihar Yobe.
Yohanna, wanda kuma Bishop na Kontagora Katolika Diocese, ya bukaci hukumar soji da ta bi shari’ar har zuwa karshenta mai ma’ana don zama abin hana wasu.
Yayin da yake Allah-wadai da kisan da sojojin suka yi, shugaban a cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun mai taimaka masa kan harkokin yada labarai, Daniel Atori, ya ce babu wanda ke da hakkin kashe ran wani.
Don haka, ya ce, “a kasar da doka ta yi aiki, ba za a amince da irin wadannan abubuwa ba.”
“Kun san da a ce gwamnatin tarayya da na Jihohi da kuma hukumomin tsaro sun yi gaggawar yin haka cikin shekaru da yawa, da an dakile irin wadannan laifuffuka da kadan.”
“Bari hukumar soji ta mika sojojin da aka kora ga ‘yan sanda domin gurfanar da su a gaban kotu,” inji shi.
Hakazalika, Dakta Bashir Yankuzo, babban Limamin Jami’ar Fasaha ta Tarayya da ke tsakiyar Masallacin Minna, ya ce matakin korar jami’an abin farin ciki ne domin hakan zai kara sahihai ga al’amuran sojojin Najeriya.
“Abin bakin ciki ne ga wanda yake sanye da kakinsa ya koma ga ba dan fashi da makami kadai amma mai kisan kai.”
“Koyarwarmu da tarbiyarmu a matsayinmu na Musulmi sun nuna mana cewa Kiristoci ba su horar da a kashe rayukan da ba su ji ba ba su gani ba, shi ya sa ba ma ganin abin da ya yi a matsayin yunkurin ruguza Musulunci.”
“Ina fata hukuncin ba zai tsaya a iya korar su ba amma Sojoji kuma za su bi diddigin yadda aka yi adalci. “
“Muna jiran doka ta dauki matakinta game da shari’ar kisan kai a gaban kotun da ta dace,” in ji shi.NAN
A wani labarin kuma Cin Zarafin Jami’an ‘Yan Sanda: IGP Ya Sha Alwashin Kamawa, Da Gurfanar Da Masu Laifi
Sufeto-Janar na ‘yan sanda, IGP Usman Alkali Baba a ranar Litinin ya yi Allah-wadai da yadda ake ci gaba da kai hare-hare kan jami’an ‘yan sanda da maza da ke sanye da kayan aiki, inda suke gudanar da ayyukansu na tabbatar da doka a sassa daban-daban na kasar nan.
IGP a cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar, CSP Olumuyiwa Adejobi ya fitar, ya jaddada cewa hare-haren da ake kaiwa jami’an ‘yan sanda, ya sabawa doka da oda.