CAN, HURIWA sun ce Elrufai ya sauka kan sace Dalibai 26
Kungiyar kiristoci ta Najeriya da kungiyar Marubutan kare hakki dan adam ta Najeriya sun bukaci gwamnan Kaduna Nasir Elrufai daya sauka kan mukaminsa saboda rashin tsaro da yayi kamari a Jahar.
Suna Kira ne saboda Gwamnan ya kasa bada cikakken tsaro, sannan Kuma yaqi yayi sulhu da Yan ta’addan.
KARANTA:Allahu Akbar, Haka lamarin Allah yake
A jiya dai Dalibai 26 ne aka dauke daga Makarantar Bathel Baptist Church, dake Maraban Rido, karamar hukumar Chukun a Jahar.
Shugaban Yan sandan Jahar ya tabbatar da aukuwar lamarin, yace Yan sanda sun bi sawun Yan ta’addan.
Shugaban CAN reshen Jahar Kaduna, Joseph Yahab, babban malamin cocin baptisma yace da akwai Dalibai dari da tamanin kamin aukuwar lamarin, sai dai a safiyar litin inda ba’a sami 174 ba.
Yayi kira ga gwamanan daya sauka tunda ya kasa samar da tsaro a Jahar. Sai dai gwamnan ya nuna rashin jindadinsa akan lamarin.