Ƙungiyar Kiristoci ta Najeriya a ranar Asabar ta koka na yadda ɗalibai 4 na Kwalejin Bethel Baptist dake Kaduna, suka shafe kwanaki 120 a hannun ƴan bindiga, bayan sun sace su watanni huɗu da suka gabata.
Ƙungiyar tayi kira ga Gwamnati da ta ruɓanya ƙwazonta wajen magance ta’addanci a ƙasar nan.
Mataimakin Ƙungiyar na Jahohin Arewa guda 19 da Abuja na Ƙasa kuma shugaban ƙungiyar a Kaduna Rev. Joseph John Hayab, ya bayyana haka a cikin wata sanarwa daya fitar.

KARANTA WANNAN LABARIN: Jam’iyyar APC tafi kowa cin hanci, bata da ƙwarewar Shugabanci — Cewar Atiku
Sanarwar tace “abin baƙin ciki ne mu tuna cewa duk da matakan tsaro da dama da Gwamnatin Kaduna ta ɗauka, amma har yanzu ƴaƴan mu na makarantar Bethel Baptist wanda aka sace tun ranar 5 ga watan juli na Shekarar 2021 a farfajiyar makarantar dake Damishi, amma har yanzu ba’a sako su ba.
“Iyaye, hukumar makarantar, da ƴan uwa sun damu matuƙa akan lamarin. Munyi addu’a, kuma muna cigaba da yi. Muna roƙo, kuma muna kuka ga gwamnati da duk wanda keda faɗa aji a ɓangaren tsaro ya sani cewa har yanzu ƴancin ƴaƴan mu ya gagara.
Haka zalika, Rundunar Ƴan Sandan Jahar Kaduna tace tana bakin ƙoƙarin ta, na ceto sauran ɗaliban ba tare da anyi masu koda rauni ne ba.
Jami’in Hulɗa da Jama’a na Rundunar ASP Mohammad Jalige a wata tattaunawa da wakilan majiyar mu, yace jami’an tsaro nayin dukkanin abinda zasu iya na ganin an ceto sauran ɗaliban, gami da kamo masu garkuwa da mutanen a inda suke a faɗin jahar.