Shugaban Ƙungiyar Kiristoci ta Najeriya reshen Jahar Kaduna Rev. John Hayab ya yabawa Rundunar Ƴan Sandan Jahar sakamakon kai wani hari da suka yi a maɓoyar ɓarayin daji, tare da kama guda biyu.
Hayab yace “CAN ta Jahar Kaduna na jinjinawa Rundunar Ƴan Sandan Jahar Kaduna da irin gagarumar nasarar da suka samu.
“Wannan shine abinda ƴan Kaduna ke ta buƙata tuntuni tare da yin addu’o’i. Muna fatan zasu cigaba da hakan har sai an magance ƴan bindiga a jahar.
KARANTA WANNAN LABARIN: Mutane 5 Ne Suka Mutu Tare Da Jikkata 21 Sakamakon Hatsarin Motar Bas A Kudancin Birnin Moscow
Wannan nasara abun a yaba ce, musamman data zo a farkon shekara.
“CAN ta Jahar Kaduna na kuma sanar da al’umma cewa biyu daga cikin ɗaliban makarantar Bethel Baptist an sako su daga inda ake tsare dasu.
“Waɗannan ɗaluban sune wanda akayi garkuwa dasu tun ranar 5 ga watan Juli a shekarar data gabata, inda uku suka yi saura, inda aka sako guda 1 a ranar Talatay28 ga watan Disamba na shekarar 2021, tare da sako wani a ranar 1 ga watan Janairun Sabuwar Shekarar 2022.
“Muna fatan zasu cigaba da wannan jajircewa domin samun nasarar kuɓuto da sauran ɗalibi, da sauran wanda suke a hannun masu garkuwa da mutane.