Canjin Kudi: Idan har halastaccen kuɗi ne da kai, ka kai shi CBN – Bashir Ahmad ga Ganduje
Bashir Ahmad, mai baiwa shugaban kasa Muhammadu Buhari shawara kan harkokin sadarwa na zamani, ya jajirce wajen ganin Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jihar Kano ya kai tsofaffin takardun kudinsa na naira zuwa babban bankin Najeriya, CBN, idan har halastacce ne.
A ranar Juma’ar da ta gabata, Ahmad yana mayar da martani ne ga Ganduje, wanda ya caccaki manufar sake fasalin Naira, ya kuma bayyana hakan a matsayin wani yunkuri na durkusar da dimokuradiyya da kuma zagon kasa ga babban zabe mai zuwa.
KARANTA WANNAN LABARIN: APC Ta Fara Siyar da Fom Din Tsayawa Takarar Gwamnan Bayelsa, Kogi, Da Imo
Ganduje ya kuma zargi Buhari da bullo da wannan manufa a jajibirin zabe, inda ya ce ya kamata ya yi a cikin shekaru bakwai da suka gabata ko kuma bayan zabe.
To sai dai kuma a martanin da Ahmad ya mayar wa Ganduje da sauran su, ya ce su daina tada zaune tsaye, su kai tsohon takardunsu na Naira ga CBN.
“Baba Dan Audu, Shugaban kasa Baba Buhari ya umarce ka da ka kai kudinka zuwa CBN. Za’a turo maka saƙo idan Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa, EFCC da Sashen Leken Asiri na Ƙasa, NFIU sun tabbatar da cewa halal ne kuɗin ka.
A wani labarin kuma: Yanzu lokacin mai dawa kura aniyar ta ne, dole Buhari ya yi wa Tinubu kamfen – Onanuga
Saura mako guda da gudanar da zaben shugaban kasa, mai magana da yawun Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen Tinubu, Shettima Bayo Onanuga, ya dage cewa shugaban nasa ya cancanci goyon bayan shugaban kasa Muhammadu Buhari.
Bayanin hakan na kunshe ne a wani sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter ranar Asabar.