Rundunar ‘yan sandan jihar Ogun a ranar Juma’a, ta gargadi masu zanga-zangar da su ke kawo cikas ga zaman lafiya a hanyar Legas zuwa Abeokuta.
Kakakin Rundunar ’Yan sandan jihar, SP Abimbola Oyeyemi, ya yi wannan gargadin a lokacin da yake zantawa da Kamfanin dillancin Labarai Kasa NAN, a Ota, da ke Ogun.
Jaridar DIMOKURADIYYA ta tattaro cewa Oyeyemi ya ce jama’a na da ‘yancin yin zanga-zanga, amma, kada su kawo cikas ga zaman lafiyar jama’a.
“‘Yan sanda ba za su bar mutane su haifar da tashin hankali ta hanyar karya a cikin jihar ba,” in ji shi.
KARANTA HAKANAN Rashin Kudi Yasa Mqsu Zanga-zanga Toshe Hanyar Legas Zuwa Abeokuta
Kakakin ya ce an tura dukkan kwamandojin ‘yan sandan yankin ne domin wanzar da zaman lafiya a hanyar Legas zuwa Abeokuta.
Jaridar Solacebace ta ruwaito cewa wasu fusatattun masu zanga-zangar sun tare manyan hanyoyin Sango-Ota, Ifo, Papa da Itori dake kan titin Legas zuwa Abeokuta, saboda kin karbar tsohon kudin naira 500 da naira 1,000 da gidajen mai suka yi.
Wakilinmu da ya bi diddigin lamarin ya lura cewa an ga masu zanga-zangar suna wasan kwallon kafa a titin mota yayin da masu ababen hawa da masu wucewa suka makale na tsawon sa’o’i.
Wani direban dan kasuwa, Mista Tope Bankole, ya ce galibin gidajen mai ne suka haddasa zanga-zangar, saboda sun ki karbar tsohuwar kudi Naira 500 da Naira 1,000.
Bankole ya ce yana da sama da Naira 130,000 daga cikin kudin Naira 1,000, inda ya ce ya yi kokarin yin amfani da wasu kudaden wajen siyan man fetur amma aka ki amincewa da tsofaffin kudaden.
A cewarsa, gidajen mai ya kamata su rika karbar wadannan tsofaffin kudade saboda direbobin da ke siyan man ba za su iya kashe kudaden a gidajen mai ba.
A Wani Labarin Kuma NBC Ta Bukaci Masu Watsa Labarai na Kasashen Waje Su Yi Rijista A Cikin Kwanaki 30
Hukumar kula da kafafen yada labarai ta Kasa (NBC), ta bukaci masu yada labarai na kasashen waje da ke da ofisoshi a Najeriya da kuma wayar da kan su a cikin kasar da su yi rajista da hukumar cikin kwanaki 30.
Babban daraktan Hukumar NBC, Malam Balarabe Ilelah, ne ya yi wannan kiran a wurin gabatar da amincewa na wucin gadi ga sabbin masu lasisi 67 da aka amince da su, ranar Juma’a a Abuja.