Canjin yanayi: Dole Ƴan Najeriya su fara amfani da keken lantarki – Kwararre
Wani masani kan sauyin yanayi da muhalli dan kasar Denmark Henrik Pedersen ya shawarci ‘yan Najeriya da su rungumi kekunan wutar lantarki domin rage tasirin sauyin yanayi.
Babban mai ba da shawara kuma manajan ayyuka a rukunin NIRAS ya zanta da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya NAN.
KARANTA WANNAN LABARIN: Mutane 12 Sun Hallaka A Wani Harin Bam Da Aka Kai Da Mota A Somaliya
Najeriya na fuskantar rudani da yanayi wanda ya yi sanadin salwantar rayukan jama’a da dama tare da raba dubbai a wasu jihohin kasar.
Pedersen ya koka da yadda sauyin yanayi ke karuwa tare da jaddada bukatar kasashe su rage fitar da hayaki mai gurbata muhalli (GHG).
Masanin ya ce yin amfani da kekuna (kekunan lantarki) na iya zama hanya mafi arha, da sauri kuma mafi dacewa da zirga-zirga.
“Idan kana tafiya a kan keke maimakon mota, to ba ka da hayaki, ko da keken lantarki ne, fitar da iska zai yi kadan a kalla.
“Har ila yau, idan aka kalli kera kekuna ba ya cin wani abu mai yawa ko kuma fitar da CO2 mai yawa (cabon dioxide) idan aka kwatanta da motoci.
“Don haka wannan ma’auni na musamman na iya yin nisa wajen magance wasu batutuwan da suka shafi yanayi, baya ga cewa hawan keke yana sa ku zama masu ƙoshin lafiya.”
Pedersen ya kara da cewa kekuna masu amfani da wutar lantarki sun fi sauri saboda yawan zirga-zirga a manyan biranen duniya.
A wani labarin kuma: Mutane 12 Sun Hallaka A Wani Harin Bam Da Aka Kai Da Mota A Somaliya
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nada Mista Aminu Umar-Sadiq a matsayin sabon Manajan Darakta na Hukumar Kula da Zuba Jari ta Najeriya NSIA.
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mai ba da shawara na musamman kan harkokin yada labarai da sadarwa ga mai girma ministan kudi, kasafin kudi da tsare-tsare na kasa, Tanko Abdullahi, a daren jiya.