Jam’iyyar PDP a ranar Juma’a ta buƙaci kotu ta bada Wani umarni ga Sanatoci uku da ƴan Majalisa 27, waɗanda suka canza sheƙa daga jam’iyyar PDP a cikin wata ƙara da suka shigar akan Gwamnan Jahar Zamfara Bello Matawalle.
PDP ta bakin lauyan ta O.J. Onoja ta shaidawa Mai Shari’a Inyang Ekwo na Babbar Kotun Tarayya Abuja, a cikin wani kuɗiri da jam’iyyar ta shigar mai suna FHC/ABJ/CS/650/2021, da aka shigar ranar 30 ga watan Satumba.
PDP ta buƙaci kotu data kori Matawalle, da Sanatoci guda uku, da ƴan Majalisar tarayya guda 6 gami da ƴan majalisun jahar da suka bar jam’iyyar PDP zuwa APC.
KARANTA WANNAN LABARIN: An Jiyo karar Fashewar wani Abu a Barikin sojin Nigeria da ke Calabar
Idan dai za’a iya tunawa, Jam’iyyar PDP ta shigar da Hukumar Zaɓe mai Zaman Kanta ƙara da APC, da Shugaban Majalisar Dattijai, da Shugaban Majalisar Wakilai, da Gwamnan Zamfara, da Babban Jojin Jahar Zamfara, a matsayin mutum 7 da tayi ƙara.
Kamfanin Dillancin Labaru na Ƙasa ya ruwaito cewar Matawalle da Sanatoci guda 3, da ƴan Majalisar tarayya guda 6 gami da dukkanin mambobin Majalisar jahar Zamfara guda 24 a ranar 29 ga watan yuni suka canja sheƙa zuwa jam’iyya mai mulki ta APC.
A yayinda mataimakin Gwamnan Mahdi Gusau yaƙi amincewa da canja sheƙa zuwa APC.
A saboda haka, Jam’iyyar PDP ta buƙaci umarnin kotu, na sanya Matawalle a matsayin na 8 da ake ƙara, tunda da farko ofishin sa kaɗai ta sanya.
Ta kuma nemi kotu ta tabbatar dacewa, ko Matawalle da ƴan majalisun nada damar cigaba da kasancewa a saman kujerun da suke akai, alhali an zaɓe su ne a wata jam’iyya.
Comments 1