Mai horas da Manchester United Ole Gunner Solskjear ya ce, Edinson Cavani ba zai sami fafata wa a wasan farko na gasar Firimiya da Kungiyar zata buga da Leeds United a gobe asabar ba.
Sai dai, Kocin bai bayyana dalilin da yasa dan wasan na kasar Yorogwai bazai, fafata a wasan ba, bayan yako koma gida ya fafata wa kasarsa a gasar Copa America, a makwanni da su ka gaba.
Kazalika ya yi karin haske dangane da yan kasar Ivory Coast wato Amad da Eric Bailly wadanda su ma, su kaje wa kasar su wasa a gasar Olympics.
KARANTA WANNAN LABARIN: Gobara ta Kone gidan Talbijin a Ogun
” Bai dade da gama zaman killace wa kan cutar Corona ba, Amma ya Dan dakata kadan ne, domin wadansu dalilai” inji Kocin na Manchester United.
“Eric da Amad suma sunje kasar su wasa, Kuma ya kamata su murmure kafin fara atisayi da sauran abokan wasansu, domin sun buga wasannin a gasar Olympics” inji shi.
Cavani ya ciwa Manchester united kwallaye 17 a kakar wasar shi na farko a kungiyar, inda 13 daga cikin su, ya zura su a watannin hudu karshe na kakar wasan.