Babban bankin ƙasa da hukumar kula da hada-hadar hannayen jari ta Nigeria sun sanyawa wasu manyan bankunan kasarnan sama da 20 takunkumi, bayan da suka aikata wasu laifuffuka daban-daban da suka hada da karya dokar musayar kudi ga yan kasuwar canji da kuma ka’idojin hana fasa-kwauri.
Bankunan sun hada da GT Bank, UBA Bank, Access Bank Plc, Stanbic IBTC Bank, da kuma Fidelity Bank Plc.
Dangane da ka’idojin tsari, ana buƙatar bankunan da aka sanyawa takunkumin da biya tarar ga hukumomin da ke kula da su, tare da samun shaida daga cikin rahoton kuɗin da aka tantance.
KARANTA WANNAN: Yan Bindiga sun sace mataimakin shugaban wata Sikandire a Abuja
Daga cikin wadanda abun ya shafa akwai bankin GT inda ya samu tara mafi girma, wanda ya kai sama da rabin naira biliyan, domin kuwa babban bankin kasa ya ci tarar bankin Naira miliyan 692, saboda saba ka’idojinta kan wasu hada-hadar kasuwanci da wasu kamfanonin na daban.
An ci tarar bankin UBA Naira miliyan 273 ne bisa wasu laifuka biyu kacal a kasuwa. An ci tarar Naira miliyan 260 saboda karyar bayanan da aka yi na sayayya a asusun wasu kwastomomi.
Hukumar ta kuma bukaci bankin da ya biya N13m don rashin tantance abokan ciniki da kuma jinkirin gabatar da rahoton hada-hadar kasuwanci.
Comments 1