Wani matashi ɗan Najeriya mai tuƙin motar haya a jihar Legas, ya koka kan ƙarancin sababbin kuɗi da kuma tsofaffin takardun N1000 da N5000 da aka ɓatar da su.
A cikin wani bidiyo da ya sanya, matashin ya ce fasinjojin sa sun kasa samun sababbin kuɗin, kuma har yanzu tsofaffin kuɗi suke bashi waɗanda aka daina amfani da su. Rahoton jaridar Legit.ng
KU KARANTA KUMA: Ku Yi Haƙuri Ku Ci Moriyar Sabon Tsarin Sauya Fasalin Kuɗi -Gwamnan CBN
Matashin ya nuna ɓacin ran sa kan lamarin. Ya bayyana cewa duk mutane basa karɓar tsofaffin kuɗin sa, fasinjojin sa sun cigaba da lafke shi da tsofaffin kuɗin.
Direban mai tuƙa motar haya ya ɗauki bidiyo lokacin da yaje gidan mai domin shan man fetur inda ya nuna motar sa da kuma fasinjojin dake ciki.
Ya roƙi gwamnan babban bankin Najeriya (CBN), Godwin Emefiele da ya kawo masa ɗauki.
2023: Miyagun Mutane Suna Amfani Da Buhari Wajen Durkusar Da APC – El-Rufai
Gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya ce shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kyale wasu mutane da ya bayyana a matsayin “mugayen mutane” su yi amfani da shi wajen yakar jam’iyyar siyasar da ta ba shi dama don bauta wa Najeriya.
Ya ce mutanen da ke amfani da shugaban kasa a matsayin makamin kayar da jam’iyyar APC na yin hakan ne saboda sun kasa yin yunkurin tilasta wa nasu dan takarar a jam’iyyar a zaben fidda gwani na watan Yuni shekarar 2022.