Babban Bankin Najeriya a ranar Juma’a ta wayar da kai tare da ƙarfafawa ƴan Najeriya akan amfani da kuɗin eNaira da sauran wasu shirye-shirye da zasu inganta tattalin arzikin Najeriya.
Gwamnan Babban Bankin Najeriya Mr Godwin Emefiele Wanda ya bayyana haka a ƙarshen taron na wuni niyya ranar Juma’a a Asaba.
Emefiele wanda ya samu wakilcin Daraktan Sadarwa na Babban Banki Mr Osita Nwasinobi, yayi kira ga ƴan Najeriya musamman waɗanda suka kammala karatu dasu shigar da kansu a shirye-shiryen Babban Bankin Najeriya.
KARANTA WANNAN LABARIN: Ɗalibai sun yi kira ga Gwamnatin Tarayya, ASUU dasu samar da matsaya a kawo karshen yajin aiki
Yace ” Taron Babban Bankin Najeriya wani gangami ne na wayar wa Al’umma kai a Asaba ta Jahar Delta akan shirye-shirye da Tsare-tsaren su.
“CBN na bada gagarumar gudummawa wajen samar da ayyukan yi, da inganta abubuwan da ake shigowa dasu, muna da shirye-shirye ga Ƴan Najeriya domin inganta tattalin arziki.