Babban bankin Kasa (CBN) ya musanta rahotannin da ake ta yadawa cewa ya ba bankunan kasuwanci izinin karbar tsoffin takardun kudi na N500 da N1,000.
A baya jaridar DIMOKURADIYYA ta ruwaito cewa a ranar Juma’a ne babban bankin kasar CBN ya umarci bankunan kasuwanci da su karbi tsofaffin takardun kudi na Naira 500 da kuma N1,000 duk da cewa bankin First Bank na Najeriya shi ma ya fitar da sanarwar yin kira ga kwastomominsa da su ajiye tsofaffin kudaden.
Sai dai a wata sanarwa da Osita Nwanisobi, Daraktan Sadarwa na Kamfanin na CBN ya fitar a ranar Juma’a ya ce rahoton karya ne ba a bada izini ba.
Ya ce babban bankin ya tsaya tsayin daka kan umarnin shugaban kasa Muhammadu Buhari na cewa kawai ya ba da damar a rika yawo da tsohuwar takardar kudi ta N200 na tsawon kwanaki 60.
“An jawo hankalin Babban Bankin Kasa kan wasu sakonni na karya kuma ba tare da izini ba da ke cewa CBN sun ba da izini ga bankunan Kasuwanci su karbi tsoffin takardun kudi na N500 da N1,000.
“Don kaucewa shakku, kuma bisa tsarin yada labarai na shugaban kasa na ranar 16 ga Fabrairu, 2023, an umurci CBN da sake fitar da tsoffin takardun kudi na N200 KAWAI kuma ana sa ran za a yi ta yawo a matsayin takardar kudi har na tsawon kwanaki 60. zuwa Afrilu 10, 2023. kamar yadda jaridar Solacebace ta rawaito
A Wani Labarin Kuma Babban bankin Kasa CBN Ya Bude Shafi Don Yin Rijistar Tsofaffin Kuɗin Naira
Babban bankin Kasa CBN ya bude shafin karbar tsofaffin takardun kudi na naira daga mutanen da har yanzu suke da takardun kudin.
Hukumar kula da harkokin banki ta bude shafin ne a shafinta na yanar gizo, kwanaki bayan da bankuna suka fara kin amincewa da tsofaffin takardun kudi .