Babban bankin Najeriya ya bayar da sabon bayani kan dawo da tsofaffin takardun kudi na Naira
Wa’adin ranar Alhamis 31 ga watan Junairu, 2023, ya kasance abin damuwa ga ‘yan Najeriya
KARANTA WANNAN LABARIN: Yadda Budurwa ‘Yar Yiwa Kasa Hidima Ke Sarrafa Kwallo Kamar Pele, Maza Sun Jinjina Mata
Hakan ya faru ne saboda galibin ‘yan Najeriya sun yi korafin cewa sun kasa samun sabbin takardun kudi
Babban Bankin Najeriya CBN ya yi karin bayani kan dawo da tsofaffin kudaden Naira a daidai lokacin da wa’adin ya ke kara kusantowa.
Ana sa ran ‘yan Najeriya za su mayar da tsohon takardun kudin Naira zuwa bankin kafin ranar 31 ga watan Janairun 2023.
A ranar Juma’a, 13 ga watan Janairu, 2023, CBN ya tunatar da ‘yan Najeriya cewa ba za a kara wa’adin ba.
Ku tuna cewa Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito CBN ya kaddamar da sabon takardun kudi na N200, N500, da N1000 a ranar 23 ga watan Nuwamba, 2022, da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi yayin da sabbin takardun kudaden suka fara yawo a ranar 15 ga watan Disambar shekarar 2022.
Sakon CBN akan tsoffin takardun kudi
CBN a cikin sakon ya tunatar da ‘yan Najeriya cewa sabbin takardun kudi na N200, N500 da N1000 za su daina zama bisa ka’ida a ranar 31 ga watan Janairun wannan shekara.
Babban sakon bankin na cewa: “Tunawa ga jama’a cewa tsofaffin jerin takardun kudi na N200, N500 da N1000 sun daina zama doka kafin ranar 31 ga watan Janairu, 2023.
An sake ba ku shawarar ku mayar da su bankinku kafin cikar wa’adin.”
A wani labarin kuma,Kogi: Atiku Yayi Alkawarin Farfado Da Kamfanin Karafa Na Ajaokuta Idan Aka Zabe Shi a 2023
Dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya ce idan aka zabe shi a zaben shugaban kasa mai zuwa, zai farfado da kamfanin karafa da ke Ajaokuta na jihar Kogi gaba daya domin samar da ayyukan yi ga dimbin matasan Najeriya.
Atiku ya bayyana hakan ne a filin wasa na confluence dake Lokoja a ranar Asabar yayin yakin neman zabensa na shugaban kasa, inda ya ce kada kuri’a a gare shi ita ce mafita ga kalubalen da gwamnatin tarayya ke fuskanta.