Wata kungiya wacce ba ta gwamnati ba dake tallafawa mata da kananan Yara mai suna CCDWCA, ta bayyana cewa ta sanya Yara 30 a makarantu daban-daban a jihar Kaduna a wani mataki na kungiyar na magance matsalolin rashin zuwa yara kanana makaranta a jihar.
Kakakin kungiyar, Malam Hamisu Alkhamees, shi ne ya bayyana hakan ga manema labarai a birnin tarayya a Abuja a ranar Litinin.
A cewarsa, tallafin na su suna lura da marasa galihu ne da ba su samu damar samun nagartaccen ilimi, tare da kuma samun wadataccen ruwan a kauyen Magwanda dake karamar hukuma Zariya.
Har wala yau ya ci gaba da cewa; sun samar da wannan tsarin ne domin tallafawa marasa galihu a Zariya, inda yara akalla 30 aka sanya su a makarantun Firamare da Sakandare, sannann ya kara da cewa; ba kawai kudin makarantarsu kungiyar ta biya ba, har lura da bukatunsu na yau da kullum kungiyarsu za ta dauki nauyi.
Sannan har wala yau, kungiyar ta ce ya zuwa yanzu suna gina rijiyoyin burtsatse a kauyen Magwanda domin ganin an tallafawa mata da kananan Yaran yankin da ba su samun damar samun ruwan sha.
Sun shawarci Iyaye da su rika amfani da tsarin kayyade iyali domin rage yawa ‘ya’yan da ba za su iya daukar nauyinsu ba domin ganin an magance matsalolin da yaran ka iya fadawa.
Har wala yau Alkhamees, ya yi kira ga shugabannin addini, da Sarakunan gargajiya da sauran masu ruwa da tsaki da su bai wa bangaren ilimi da lafiya muhimmanci tare da samar wa al’umma hanyoyin samun ruwan sha cikin sauki.