Hukumar kashe gobara reshen jihar Kano tace ta ceto rayuwar wani matashi mai suna Mohammed Haladu, dan shekaru 30 a duniya da ya fada rijiya a unguwar Kofar Ruwa dake karamar hukumar Dala a Kano.
Alhaji Saidu Muhammad, wanda shi ne kakakin hukumar ya tabbatarwa da menama labarai faruwar lamarin a ranar Alhamis.
Yace matashin yaje gyara rijiyar ne wanda tsautsayi ya kwashe sa ya fada ciki, amma an yi nasarar ceto sa.
“Bayan ceto matashin kun damka sa a hannun dan uwansa Malam Aliyu Iliyasu mazaunin unguwar Kofar Ruwa.”
https://dimokuradiyya.com.ng/masu-kashe-gobara-sun-ceto-rayuwar-wasu-mutane-uku-a-kano/
Muhammad yace, wani Mutum ne mai suna Mal Nasiru Abdullahi ya musu kiran agaji tare da shaida musu Haladu ya fada rijiya.
“Da muka samu rahoton abinda ke faruwa bamu wani bata lokaci ba wajen tura jami’anmu, kuma an samu nasarar ceto rayuwarsa”.
Jami’in yaja hankalin iyayen da suke da rijiya a gida cewa, su tabbatar da an rufe rijiyoyin da murfi saboda kula da rayuwar yara.