Gamayyar Kungiyoyin Arewa (CNG), reshen daliban jihar Kaduna, sun ce za su tsayar da al’amuran cake a Zariya idan ba a dauki matakin ganin an sako mutanen nan da Akayi garkuwa da su a ranar Litinin ba, Nan da kwanaki bakwai.
A wata sanarwa da kodinetan jihar Kaduna, Jamilu Musa ya sanyawa hannu, daliban sun ce gwamnatin tarayya da na jihohi sun gaza wajen samar da tsaron lafiyar jama’a da tsaron rayuka da dukiyoyin ‘yan Najeriya.
KARANTA WANNAN LABARIN: Buhari Ya Isa Paris Domin Taron Zaman Lafiya
“Mun lura da cewa a cikin matan da aka yi garkuwa da su a karamar hukumar Zariya akwai uyayen dalibai da dama a makarantu daban-daban.”
“Yayin da muke jin radadin iyalai da abokan arziki da ‘yan uwan ma’aikatan da aka yi garkuwa da su, muna bukatar hukumomin da abin ya shafa da su dauki matakin gaggawa domin a sako su a raye, da kuma gwamnati ta kara nuna himma wajen kare rayukan ‘yan kasa. da dukiyoyin su.”
A wani labari dake da alaka da wannan
Darakta, ilimi da ci gaban zamantakewa na karamar hukumar Zariya, Misis Deborah Mugu; tace Wasu ‘yan bindiga sun yi garkuwa da mataimakinta, Dalhatu Aliyu-Awai tare da wasu ma’aikata 11 a garin Kidandan da ke karamar hukumar Giwa ta jihar Kaduna a ranar Litinin.
Wata majiyar tsaro ta shaida wa jaridar Daily Trust cewa wadanda abin ya shafa na dawowa ne daga ziyarar jaje da wani ma’aikacin Karamar hukumar ya rasa mahaifinsa a lokacin da ‘yan bindiga suka tare su, da misalin karfe 1:30 na rana.
Majiyar Jaridar Dimokuradiyya ta ruwaito cewa, ’yan bindigar sun sako Umar Abubakar (Katako) direban motar bas mai dauke da mutane 18, inda suka bukaci ya koma gida ya sanar da ‘yan uwa cewa, an yi awon gaba da wasu ma’aikatan.
Ya ce bisa ga rahoton da ya faru a kan idonsa, ‘yan bindiga 6 dauke da AK47 sun dira motar bas din mintuna 45 bayan ta taso daga garin Kaya. Ya ce bayan sun yi bincike tare da kwashe fasinjojin da kayayyakin masu daraja, inda ‘yan bindigan sun kai su wani yanki na daji.
Ya lissafa sauran wadanda abin ya shafa kamar haka: Sulaiman Zailani, Nura Abdullahi, Umar Shehu, Halima Tabari, Fatima Abdullahi da Hafsat Zakari.
Sauran sun hada da Maryam D, Hulaila Fate, Hajara Muhammad, Kuluwa Isa da Amina Sulaiman.
Comments 1