Jamhuriyar Chadi ta nemi hadin gwiwa da gwamnatin Najeriya domin hada hanyar samar da wutar lantarkin ta da na Najeriya.
Jakadan kasar Chadi a Najeriya, Abakar Saleh Chahaimi ne ya bayyana haka a lokacin da ya ziyarci ministan wutar lantarki, Engr. Abubakar Aliyu a Abuja.
Ya kuma ce an taba yin hulda da mu’amala a baya kan hada-hadar wutar lantarki tsakanin gwamnatin Chadi da Najeriya wanda bai kai ga rattaba hannu kan yarjejeniyar fahimtar juna ba.
Sai dai Abakar, ya bukaci ministan da ya sake bude shirin hadin gwiwa a tsakanin kasashen biyu, inda ya bayyana cewa, kasashen biyu sun ci gajiyar hadin gwiwar.
Ya ba da misali da alakar wutar lantarki da aka samu a baya-bayan nan tsakanin Chadi da Kamaru wanda bankin duniya ya samar, inda ya ce Najeriya za ta iya yin irinsa da kasar Chadi domin inganta dunkulewar kasashen Afirka domin samun ci gaba.
A nasa bangaren, ministan wutar lantarki, Engr. Aliyu, ya ba da tabbacin cewa za a ci gaba da yin cudanya kan huldar wutar lantarki da kasar Chadi yayin da Najeriya ta himmatu wajen hada kan yankin.
Ministan ya kuma ce daraktoci a Ma’aikatar Wutar Lantarki tare da hukumomin za su fara huldar a tsakanin kasashen biyu.