Akwai alamun cewa ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Chelsea dake ƙasar Ingila a ƙarƙashin jagorancin mai horas wa Frank Lampard ta gano matsalar da taje damun ƙungiyar a dukkanin wasannin baya da aka dinga zabgawa Chelsea ƙwallaye tako ina a raga.
Sun gano matsalar ne ta dabarar da sukayi suka sayo mai tsaron gidan da baya bari a sakamasa ƙwallo a zare wato Eduard Mendy domin gyara na musamman.
Chelsea dai ta kasance musan kowanne wasa a baya sai an jefamata ƙwallo a zare koda zatayi nasara. Amma daga zuwan wannan mai tsaron gidan yanzu ya kama wasanni guda 6 ba tare da anjefamasa ƙwallo a zare ba. Koda a wasan da ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Chelsea ta fafata a jiya a gasar zakarun nahiyar turai ba a jefamasa ƙwallo ba wato wasan da ƙungiyar ta Chelsea ta ragargaza Rennes daci 3 da nema.
Chelsea dai ta kashe manyan kuɗaɗe a kakar wasa ta bana wajen sayen ‘yan wasa inda za a iya cewa da alama kwalliya ta fara biyan kudin sabulu duba da yadda Chelsea ta fara warwarewa.