Kungiyar Kwallon kafa ta Chelsea ta kammala daukar Saul Niguez daga Madrid a yarjejeniyar aro na tsawon kaka guda. Tare da zamin siyan Dan wasan tsakiyan idan tana da sha’awa yin hakan.
Real Madrid ta kasa shawo kan Paris St-Germain da sabon tayin da ta yi na yuro miliyan 220 (fam miliyan 189) a kan dan wasan gabanta Kylian Mbappe, mai shekara 22.
Yanzu ke nan dan wasan na Faransa yana da damar ya tattauna da Real Madrid a watan Janairu kan sharuddan kwantiraginsa, kafin ya tafi can idan ya ga dama, domin a lokacin lokacinsa a PSG ya kare, a bazara mai zuwa. (Goal)
Tottenham ba ta kara tayin da ta yi wa dan gaba na gefe na Wolves Adama Traore, bayan da kungiyar ta ki sallama shi fam miliyan 30 ba a ranar Litinin. Ita dai Wolves ta bukaci fam miliyan 50 ne a kan dan Sifaniyar mai shekara 25.(Athletic)
Dan gaban Manchester United, dan Faransa Anthony Martial, mai shekara 25, ya ki yarda ya koma Lyon a tattaunawar dab da rufe kasuwar sayar da ‘yan wasa. (L’Equipe)
Sai dai ba kamar Martial, ba, domin kuwa shi dan wasan tsakiya na United Donny van de Beek, mai shekara 24, ya so barin Old Trafford amma Ole Gunnar Solskjaer ya ki yarda da tafiyar dan kwallon na Holland aro zuwa Everton. (AD).
Atletico Madrid ta yi watsi da tayin fam miliyan 18 da Manchester United ta yi wa dan bayanta dan Ingila Kieran Trippier, mai shekara 30, abin da ya sa nan da nan Manchester United, ita ma ta dakatar da tafiyar dan bayanta Diogo Dalot mai shekara 22, dan Portugal zuwa Borussia Dortmund. (Sport1)
Comments 1