Kungiyar Kwallon Kafa ta Chelsea ta kawo karshen mafarkin Manchester City na lashe kofuna hudu a kakar bana kawai bayan da ta yi waje rod da ita a gasar FA da ci 1:0.
Kwallon da Hakim Ziyech ya zura shi ya baiwa Chelsea damar zuwa wasan karshe a gasar shekara biyi a jere.
Yanzu haka wannan nasara ta Chelsea na ya tabbatar da cewa City fa ba za ta zarce da kofin ba Kenan.
Kazalika kashin da tawagar Pep Guardiola ta sha ya zama cewa ba zata lashe kofuna hudu da ta yi hari ba Kenan, to amma akwai damar lashe kofin kalubale na Carabao a mako mai zuwa a wasan karshe tsakanin ta Tottenham.
Tun a mintuna shida ne dan wasan Chelsea Hakim Ziyech ya taba lilo, to sai dai an haramta kwallon bayan aka chafke Timo Werner ya yi sater gida.