Kungiyar kwallon kafa ta Chelsea ta amince da yarjejeniyar siyan dan wasan gaban kungiyar RB Leipzig dake buga gasar Bundesliga ta kasar Jamus. Majiyarmu ta tabbatar da hakan ne a ranar Alhamis.
Rahotan ya bayyana cewa an siya Werner akan Dala miliyan 62.4, inda kuma kungiyar za ta rika biyansa Fam dubu dari biyu a duk mako.
Matashin dan wasan mai shekara 24 shi ne na biyu wanda ya fi kowa cin kwallo a gasar Bundesliga a kakar wasa ta bana da kwallo 25. Inda Lewandowski ne kawai ya fi shi cin kwallo da kwallo hudu a gabansa.