A yayin da ake gab da karkare taron manyan kasashe bakwai da suka fi karfin tattalin arziki wato G7, kasar China ta gargadi taron cewa yanzu lokaci ya wuce fa wata yar mitsitsiyar kasa zata rika juya duniya.
Wannan gargadi da ya fito daga kakakin ofishin Jakadancin kasar ta China a Birtaniya, yazo ne daidai lokacin da taron ke kokarin yiwa china mamaya.
Kasashen su aza wata gidauniya dake da aniyar kawar da karfin ikon china a bangaren tattalin arziki.
Shugaban kasar Amurka Joe Biden na daga shugabannin dake cewa lokaci ya yi ds kasashen yamma za su tashi tsaye fon tunkude kasar daga wannan dabi’a tata.
Ana sa ran cewa yayin rufe taron a ranar Lahadi kungiyar ta G7 za ta bullo da wata hanya ta taimakawa ƙasashe masu tasowa don yaki da dumamar yanayi a ƙasashen su.