A cikin wannan lokacin ne cibiyar nazarin sinadarai ta kasa NARICT ‘National Research institute for Chemical Technology’ dake Zariya jihar Kaduna ta shelanta kirkiro maganin wanke hannu(Hand Sanittizer) na rigakafin kamuwa da tutar korona Bairos dake daukar rayukar al’ummar a fadin duniya baki daya Mai lakabi da.
Antimicrobil, Antifungal & Antiviral Nanosilver Disinfectant Sanitizer ((Nanosilver particle, Na0CI, Hz02)
Bubban daraktan cibiyar ne Farfesa Jeffrey T.Barminas,ya tabbatar da cewa tuni cibiyar ta dukufa wajan fitar da Nigeriya kunya a bangaren bicike na magunguna rigakafin kwayar cutar korana Bairos.
Wannan furucin ya fito ne daidai lokacin da bubban daraktan cibiyayar ta NARICT ke karban bakuncin majalisar matasa ta kasa wato National Youth Council of Nigeriya NYCN reshen jihar Kaduna karkashin jagorancin Kwamret Jibil Suleman Salihi .
Farfesa Jeffrey ya kara da cewa, kirkiro wannan sinadari nadaga cikin gudummawar cibiyar ga kokarin murkushe kwayar cutar korona Bairos wanda ake so duk wani mai bincike ya kamata yayi don taimakon al’ummar kasa Baki daya.
Kuma yace karfafa irin wannan aiki da cibiyar tayi zai bayar da gudummawar mai yawa a bangaren samawa matasa aikin yi da samun haraji ga Gwamnati a bangarori da dama.
Ya kuma karkare da cewa a halin yanzu a duk fadin Afrika ta kudu kaf babu wata cibiya data kirkiro da maganin wanke hannu na rigakafin kwayar cutar korana Bairos kamar Wanda suka kirkira a halin yanzu.
Yace cibiyar tasa kwarewa wajan kirkiram wannan magani kuma ya tabbatar da cewa shirye cibiyar take wajan bayar dashi so inadarin ga gwnatoci ko Yan kasuwa don isar dashi ga Jama’a sai dai Sugaban ya koka wajan matsalar kudi da Shirin nasu ke fuskanta yace da fatan Gwamnati zata Basu goyan baya wajan inganta Shirin don taimakon rayukar Jama’a.
Bayan gabatar da jawabin shugabanne sai Kuma shugaban majalisar na Matasan kwamret Jibil Suleman Salihi ya jagoranci yayan majalisar tare da sauran Jama’a don ganewa idonsu kalar maganin tare da sauraren masana a bagaren kirkiran maganin da suke a cibiyar.
Bayan Jama’a sun gani kuma sunji irin ingancin sinadarin na wanke hannu da na fedawa a daki sai shugaban majalisar ya gabatar da jawabin goyan baya Inda ya tabbatar wa cibiyar cewa majalisar matasa sun gamsu da ingancin sinadarin Kuma yace zasu kai samfari ga shugabanne makarantu don yin amfani dashi ga daluban musamman yadda ganin yadda Gwamnati ta fitar da ranar komawa makarata.
Kuma ya jinjinawa cibiyar ta NARICT bisa daukar matakai na kariya yayin da ake cikin kulle na kaucewa yaduwar cutar a fadin Kasa baki daya.
A karshe Shugaban cibiyar ta NARICT ya bayar da tallafin sinadarin wanke hannu dana fesawa a daki mai yawa ga tawagar majalisar matasan don su mikashi ga al’ummar kasa Baki daya a matsayin su na wakilan al’umma.
Anyi taron lafiya an tashi lafiya.