Cibiyar Nazarin Dimokaradiyya ta Aminu Kano karkashin Jami’ar Bayero Kano ta cika shekaru 21 da kafuwarta.
Jaridar Dimokuradiyya ta ruwaito cewa, cibiyar nazarin Dimukuradiyya na Malam Aminu Kano, gidan Mambayya Kano, an kafa shi ne a watan Nuwamba 2000 a matsayin sashin bincike da horaswa na Jami’ar Bayero Kano, a cikin harabar da rusasshiyar Cibiyar Nazarin Dimokaradiyya (CDS), wanda gwamnatin tarayya ta kafa a shekarar 1989 da ta gabata.
Sai dai a lokacin da aka soke CDS a shekarar 1996, gwamnatin tarayya ta bayar da tallafin ginin ga Jami’ar Bayero ta Kano. Wanda Sakataren gwamnatin tarayya na lokacin Alhaji Gidado Idris ya mika gidan Mambayya ga tsohon mataimakin shugaban jami’ar Bayero Kano Farfesa Musa Abdullahi a ranar 3 ga Maris, na shekarar 1999.
A wata sanarwa a ranar Lahadi, mai dauke da sa hannun Daraktan gidan Mambayya, Farfesa Isma’ila M. Zango, ta ce mataki na farko daga cikin ayyukan da aka tsara don gudanar da bikin babban taron jama’a da aka shirya gudanarwa mai taken “Dimokradiyya, da kyakkyawan shugabanci da kuma tambaya kasamu hadin kan kasa”. Gwamnan Jihar Ekiti Dr. Kayode Fayemi, ya gabatar da shi a ranar Asabar, 4 ga Disamba, 2021 a dakin taro na Sa’adu Zungur Mambayya House dake Kano.
Sanarwar ta ce cibiyar da aka fi sani da Mambayya House ta shafe shekaru 2 da shekara tana gudanar da laccoci 78 da bincike 29 da horaswa 85 da kuma Wallafawa 72.
Sanarwar ta ci gaba da cewa, ”Haka kuma abun da za a gani a yayin bikin babban taron shi ne gabatar da littafi kan rayuwar fitaccen malamin nan na kasa Marigayi Yusuf Maitama Sule.
Sanarwar ta kara da cewa, shugaban taron shi ne gwamnan jihar Jigawa, Alhaji Muhammad Badaru Abubakar da babban bako na musamman shi ne shugaban kwamiti na majalisar dattawa kan muhalli Sanata Ike Ekweremadu, yayin da mai masaukin baki shi ne mataimakin shugaban jami’ar Bayero ta Kano, Farfesa Sagir Adamu Abbas.
Sanarwar ta ce, tsofaffin Daraktocin Cibiyar tun daga shekarar 2000 zuwa yanzu kamar Farfesa Attahiru Jega, da Farfesa MD Suleiman, da Marigayi Farfesa Haruna Wakili da Marigayi Farfesa Shehu Dalhatu duk an ba su kyaitar takardar karramawa.