Farfesa Promise Mebine, Babban Darakta na Cibiyar Lissafi ta Kasa (NMC), ya ce cibiyar ta horar da malaman lissafi kusan 300 a cikin shekara guda da ya yi a kan karagar mulki.
Mebine ya bayyana hakan ne a cikin wata takarda da aka ajkewa Kamfanin Dillancin Labarai na Kasa ranar Alhamis din nan a Abuja.
Ya yi nuni da cewa, an horas da jimillar malaman lissafi 300 a Calabar, Cross River da Yenagoa a Bayelsa, 150 kowannensu, domin kara kwazo a fannin darussan
A cewarsa, cibiyar ta gudanar da gasar lissafin yara mata da yara Maza a fadin kasar, bisa tsarin ci gaba mai dorewa (SDGs).
Karanta kuma: Sashen Koyon Aikin Jinya Na Jami’ar A. B. U Na Cikin Garari
“Ba a bar manyan makarantun gaba da sakandare ba a yunkurin sake mayar da nazarin ilmin lissafi a kasar nan, domin an shirya horaswa daban-daban domin nuna muhimman abubuwa a fannin.
“Haɓakawa ga membobin ma’aikata, abubuwan more rayuwa na zahiri, ci gaban fasahar Sadarwa (ICT), dakin ajiye litattafai da jin daɗin ma’aikata, suma an mayar da hankali kan su.
“Cibiyar ta samu gagarumin sauyi a ayyukanta, wadanda suka shafi inganta koyo da ilimin lissafi a dukkan matakai na tsarin ilimi a kasar nan.
“Wani abin lura daga cikin nasarorin da aka samu shine, la’akari da mahimmancin ilimin lissafi da aikace-aikacensa tare da karancin masana ilimin lissafi a kasar,” in ji shi.
Ya ci gaba da cewa, a karkashin jagorancinsa, an gudanar da tarukan karawa juna sani na wata-wata kan kimiyya, fasaha, injiniyanci, lissafi da ilimin fasaha da sana’a.
A cewarsa, an shirya horaswar ne daidai da shirye-shiryen cibiyar.
“Har ila yau, cibiyar tana gudanar da jarrabawar gasar Olympics ta kasa da kuma halartar Najeriya a gasar Olympics daban-daban,” in ji shi.
Ya jera wasannin Olympics a matsayin Olympiad Pan African Mathematics, Olympiad International Mathematics, International Physics Olympiad, International Chemistry Olympiad, International Biology Olympiad da International Olympiad in Informatics.
A cewarsa, ya kamata a lura cewa Najeriya ta samu lambobin yabo guda uku; lambar zinare da tagulla biyu a gasar Olympics ta kasa da kasa ta bana.
NAN ta ruwaito cewa an nada Mebine a matsayin Darakta/Babban Darakta na 7, na cibiyar NMC a ranar 5 ga Satumba, na shekarar 2021.
A wani labarin kuma: Rashin Tsaro: Ku Yi Imani Da Sojoji, Buhari Ya Bukaci ‘Yan Najeriya
Shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Alhamis din nan a jihar Legas ya bukaci ‘yan Najeriya da su yi imani da karfin da sojojin kasar ke da shi wajen kiyayewa da samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a kasar.
Da yake bayyana buda wasannin sojojin ruwa na Najeriya karo na 12, na LAGOS 2022, shugaban kasar ya tabbatar wa ‘yan Najeriya cewa dakarun sojin kasar za su ci gaba da gudanar da ayyukansu na tsawon lokaci domin dakile kalubalen tsaro a kasar.