A ranar Juma’a ne aka gudanar da jadawalin wasan kusa da na karshe na gasar cin kofin kungiyoyin Turai ta UEFA Europa a birnin Nyon na kasar Switzerland.
An watsa zanen kai tsaye ta shafin yanar gizon UEFA daga karfe 1:30 na rana.
A ranakun 28 ga Afrilu da kuma 5 ga watan Mayu ne za a yi wasannin kusa da na karshe na farko da na biyu.
A kasa akwai yadda aka tsara wannan jadawali na wasannin kusa da na karshe a gasar Europa:
Leipzig/Atalanta vs Braga vs Rangers
West Ham / Lyon vs Eintracht Frankfurt / Barcelona.
A wani labarin Kuma na daban.
Goma daga cikin mambobi 12 na Kwamitin Kula da Tsare-tsaren Taro na Musamman (CECPC) a jiya sun kada kuri’ar rashin amincewa da Sakataren kwamitin, Sanata John James Akpanudoedehe.
Sakataren ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ya fitar na soke kananan kwamitocin da mukaddashin shugaban kwamitin Abubakar Sani Bello ya kafa a makon jiya. Ya fito da sabon saitin bangarori.
Akpanudoedehe ya ce kananan kwamitocin da ya sanar sun maye gurbin jerin sunayen farko.
Sa’o’i kadan bayan wata sanarwa, Shugaban riko Buni ya musanta jerin sunayen.
Ya kuma nanata cewa duk ayyukan da mukaddashin shugaban ya yi lokacin da ba ya nan suna da inganci.
Kwamitin riko na jam’iyyar APC, ta hanyar sanarwar da aka fitar a ranar 8 ga watan watan Maris, da rinjayen mambobin kwamitin sun kada kuri’ar rashin amincewa da Akpanudoedehe.
Sanarwar ta samu sa hannun Gwamna Abubakar Sani Bello da Sanata Ken Nnamani da Sanata Yusuf Abubakar Yusuf da Farfesa Tahir Mammah da Sanata Abba Alli da Mista David Lyon da Akinremi Olàide da Mrs Stella Okotete da Mista Ismaeel Ahmad da kuma Dokta James Lalu.
Ta ce korar Akpanudoedehe an yi shi ne a karkashin doka ta 17 karamin sashe na 5 na kundin tsarin mulkin jam’iyyar APC, wanda ya bai wa akasarin duk wani kwamitin rikon kwarya na jam’iyyar damar kada kuri’ar yanke kauna ga duk dan majalisar da aka samu yana so.
Sakataren ya kasance ba ya nan a yawancin tarurrukan CECPC a cikin kwanaki biyun da suka gabata kuma wannan ba zai rasa nasaba da sanarwar da aka samu kwanan nan mai kwanan wata 8 ga watan Maris, 2022.
An tattaro cewa kwamitin mai mutane 10 a taron da suka yi a Lodge a jihar Neja a jiya ya yanke shawarar dagewa kan korar sakataren wanda suka zarga da rashin biyayya ga hukumar yayin da shugaban ba ya nan.