Daga: Abbas Yakubu Yaura
Gwamnan Enugu Ifeanyi Ugwuanyi ya taya Al’ummar jihar murnar cika shekaru 31 da kafuwarta tare da nuna matukar godiya ga iyayen da suka kafa ta bisa hangen nesa da karewa da jajircewarsu wajen samar da jihar.
Da yake kwatanta iyayen da suka kafata a matsayin “jarumai na gaskiya”, gwamnan ya ba su tabbacin cewa sadaukarwar da suka yi ba za ta kasance a banza ba.
KARANTA WANNAN LABARIN:Gwamna Buni Na Murnar Cikar Jihar Yobe Shekaru 31, Ya Jinjinawa Shugabannin Da Suka Shude
Gwamna Ugwuanyi wanda sakataren gwamnatin jihar, Farfesa Simon Uchenna Ortuanya ya wakilta a wajen bikin a gidan gwamnatin jihar ya taya al’ummar jihar murnar zagayowar wannan rana.
Al’ummar Enugu a bikin cika shekaru 31 da kafa jihar, inda suka yabawa mambobin kungiyar ESDA bisa wannan bikin da suka yi.
Don haka ya bukaci al’ummar jihar da su ci gaba da kasancewa da fata kuma su dage wajen addu’o’i da hadin kai, yana mai tabbatar da cewa gwamnatin jihar za ta ci gaba da tafiya a kan turbar zaman lafiya, tsaro, ci gaba da samar da ababen more rayuwa.
Wadanda suka halarci wajen bikini sun hada Mamba mai wakiltar mazabar Nkanu ta gabas Rt.Hon. Paul Nnajiofor, Shugaban Majalisar Sarakunan Gargajiya ta Jihar Enugu, HRH Igwe Amb. Lawrence Agubuzu, mataimakin shugaban majalisar, HRH Igwe Dr. Julius Nnaji, mai ba gwamna shawara na musamman kan jarkokin yada labarai, Steve Oruruo, da takwaransa na noma, Engr. Michael Ogbuekwe.
Sauran sun hada da Shugaban Hukumar Kula da Makarantun Kimiyya da Fasaha (STVSMB) Dr. G.O.C Ajah da Manajan Shirye-Shirye na Shirin Bunkasa Aikin Gona na Jihar Enugu (ENADEP), Dokta Ogbonna Onyeisi, da sauran manyan baki ne suka halarci wajen taron.
Buhari Ya Ja Hankalin Duniya Kan Ambaliyar Ruwan Pakistan Data Shafi Mutane Kusan Miliyan 30
A wani labarin kuma Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ja hankalin duniya game da ambaliyar ruwan data afku a kasar Pakistan
Shugaban kasar, a wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Garba Shehu ya fitar a ranar Asabar, ya jajantawa yadda ambaliyar ruwan teku ta bayyana a matsayin bala’i mafi muni a tarihin kasar.