Cikar Shekaru 60: Ka cigaba da yiwa Najeriya aiki – Buhari ga Gbajabiamila
Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari yayi kira ga shugaban Majalisar Wakilai na Ƙasa Femi Gbajabiamila daya kasance mai kishin ƙasa daya ke yi, tare da cigaba yiwa Nijeriya aiki kamar yadda yake yi.
Buhari yayi jawabi a wata addu’a ta musamman da aka shirya domin karrama Shugaban Majalisar akan cikar sa shekaru 69 a masallacin Ansar-Ud-Deen dake Wuse 2 a Abuja a ranar Asabar.
KARANTA WANNAN LABARIN: Matawalle ya umarci Mazauna Zamfara dasu ɗauki Makamai su kare kansu akan ƴan bindiga
Shugaban Kasar wanda ya samu wakilcin Shugaban Ma’aikatan sa Farfesa Ibrahim Gambari, yayi kira a gares shi daya cigaba da yiwa Kasar aiki, yana mai Gbajabiamila a matsayin sa na Shugaban Majalisar Wakilai ya canja yadda mutane suka fahimci Majalisar da Sashen Majalisar Zartaswa.
A jawabin sa, Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa a Jam’iyyar APC Asiwaju Bola Tinubu ya bayyana Shugaban Majalisa Gbajabiamila a matsayin mai kishin Kasa da yayi amfani da muƙamin sa wajen inganta Kyakkyawan Shugabanci a Nijeriya.
Tinubu wanda shine Jigon Jam’iyyar APC na Ƙasa, yace Allah ya sanya Shugaban Majalisa ya bada gagarumar gudunmuwa wajen inganta rayuwar ƴan Najeriya ta hanyar Majalisar