Hukumar lafiya ta duniya WHO ta ce yawan wadanda annobar korona ke halakawa gami da masu kamuwa da cutar a duk rana a fadin duniya ya karu zuwa adadin da ba a taba gani ba cikin watanni, tun bayan bullar annobar daga Chana a watan Disambar bara.
Alkalumman hukumar lafiya ta duniya a ranar Asabar sun nuna cewar, cikin awa 24, mutane dubu 259 da 848 suka kamu da cutar, inda kaso mafi yawa kuma ya fito ne daga kasashen Amurka, Brazil, Indiya da kuma Afrika ta Kudu.
A Juma’ar da ta gabata kuwa, hukumar lafiyar ta ce jumillar mutane dubu 237 da 743 suka kamu da cutar yayin da wasu dubu 7 da 360 suka mutu rana guda a sassan duniya, adadi mafi yawa tun bayan 10 ga watan Mayu.