Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da kuma ba da umarnin aiwatar da shirin inganta albashi da jin dadin ma’aikatan shari’a cikin gaggawa. Kamar yadda Daily Trust ta ruwaito
Shugaba Buhari ya sanar da hakan ne a yayin bikin kaddamar da makarantar Nabo Graham-Douglass, makarantar koyon aikin lauya ta Najeriya da ke Fatakwal a jihar Rivers ga majalisar ilimin shari’a a jiya.
KARANTA WANNAN LABARIN: Hukuncin Da Aka Yankemun Yayi Tsauri Da Yawa—Lewandowski
Buhari wanda Babban Lauyan Tarayya (AGF) kuma Ministan Shari’a, Abubakar Malami, Babban Lauyan Najeriya (SAN) ya wakilta, ya umurci shugaban hukumar tattara kudaden shiga da rabon kudi da kuma Babban Lauyan Gwamnatin Tarayya da su gaggauta fara daukar matakai don magance matsalar. fahimta da aiwatar da ingantaccen tsarin albashi da walwala ga jami’an shari’a a kasar nan.
Wata sanarwa da mai taimaka wa Malami kan harkokin yada labarai, Dakta Umar Gwandu ya fitar, ta ruwaito shugaban kasa na shirin karfafa kwazo da ‘yancin kai na bangaren shari’a, wanda ya ce ya kasance ginshikin da kwanciyar hankali ga dimokradiyyar kasar nan.
“Saboda haka, wannan gwamnatin za ta ci gaba da bayar da goyon baya ga kokarin da ake yi na sauya tsarin shari’a a matsayin wani muhimmin dabarun tabbatar da adalci, ci gaba da wadata al’umma, tare da bin doka da oda a matsayin ginshikinta,” in ji shi.
Shugaban ya kuma yi kira ga bangaren shari’a da su ci gaba da kiyaye da’ar sana’arsu tare da gudanar da ayyukansu cikin gaskiya da sanin yakamata wajen gudanar da ayyukansu na shari’a da gudanarwa.
A WANI LABARIN KUMA: Ku Yi Sulhu Da Peter Obi Da Wike, Kafin Zaben 2023 — Kiran Fayose Ga PDP
Tsohon gwamnan jihar Ekiti, Ayodele Fayose, ya bukaci jam’iyyar PDP da ta tattauna da , dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour Party, LP Peter Obi gabanin zaben 2023. Kamar yadda Daiky Post ta ruwaito.
Fayose ya kuma bukaci shugabannin PDP da su sasanta rikicin da ke tsakanin Gwamna Nyesom Wike na Rivers da jam’iyyar