Gwamna Nyesom Ezenwo Wike na Jihar Ribas a ranar Juma’a ya karbi bakuncin Mai alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammadu Sa’ad Abubakar.
Sultan ya ziyarci gidan Ada George dake fatakwal na Wike jim kadan bayan ya isa filin jirgin sama na Fatakwal.
KARANTA WANNAN LABARIN: Da Dumi-duminsa: An Dage Wasannin Premier League Na Ingila, Don Girmama Marigayiya Sarauniya Elizabeth Il
Fitattun shugabannin biyu sun yi wata ganawar sirri.
Jaridar DIMOKURADIYYA ta rawaito cewa Sa’ad Abubakar ya je Fatakwal ne domin kaddamar da kungiyar Mata Musulmi ta Najeriya (FOMWAN) karo na 37 ta shekara-shekara.
A wani labarin kuma, Yajin Aikin ASUU: Dalibin Likitanci A Shekarar Karshe Ya Zama Mai Siyar Da Abinci
Malam Usman Abubakar-Rimi, wanda dalibi ne a shekarar karshe a fannin likitanci da tiyata a Jami’ar Usmanu Danfodiyo da ke Sokoto (UDUS), ya koma mai siyar da abinci a kan titi saboda tsawaitar yajin aikin da malaman jami’ar suke yi.
A wata hira da kamfanin dillancin labarai na Kasa (NAN) a ranar Juma’ar nan a Sokoto, Abubakar-Rimi ya ce ya dauki wannan matakin ne domin su samu rayuwa mai inganci yayin da yajin aikin ya tilastawa dalibai barin makaranta.