Gwamnonin PDP sun tafi Ƙasar Spain, sun ziyarci Filin wasan Ƙwallo na Real Madrid
Domin ka ɗauki wani lokacin aiki kahuta, Wasu Gwamnoni da aka zaɓa a ƙarƙashin inuwar Jam’iyyar PDP, sun tsiri tafiya zuwa Ƙasar Sifaniya.
Gwamnonin, wanda suka yi shiga iri ɗaya, an gansu cikin nishaɗi, a yayin da suka tsaya domin ɗaukar su hoto a filin wasan Ƙwallon Ƙafa na Santiago Bernaéuare.
KARANTA WANNAN LABARIN: Wasu Kungiyoyi A jihar Bauchi Suna Neman Da Akawo Canje-canjen Halaye Akan Laifin Aikata Fyaɗe
Daga cikin Gwamnonin akwai Seyi Makinde Gwamnan Jahar Oyo, da Ahmadu Fintiri, Gwamnan jihar Adamawa, da Nyesom Wike, Gwamnan jihar Rivers, da Samuel Ortom Gwamnan Jahar Benue, tare da kuma Gwamnan Abia Okezie Ikpeazu Gwamnan Jahar Abia.
Har yanzu dai ba’a san kowane lokaci suka yi tafiyar ba, ga hotunan su nan: