By Abbas Yakubu Yaura
Labarai cikin hotuna wanda ya kafa kuma babban Fasto na cocin Salvation Ministries dake Fatakwal David Ibiyeomie a ranar Larabar da ta gabata ya ziyarci wadanda wani bangare na ginin cocin ya rufta akan su a unguwar Okpanam da ke karamar hukumar Oshimili ta Arewa a jihar Delta.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa ginin cocin Salvation Ministries da wasu ofisoshi sun ruguje yayin gudanar da hidima a yammacin ranar Talata.