Darkta-Janar ta Hukumar Kula da Kasuwanci ta Duniya kuma ƴar Najeriya, Ngozi Okonjo-Iweala ta haɗu da Shugaban Ƙasar Amurka Joe Biden a taron ƙasashe masu ƙarfin faɗa aji na G20 a Rome.
Okonjo-Iweala Wanda ta tura hotuna daga taron, tace tana amfani da damar wajen nuna godiya ga Ƙasar Amurka a bisa magani da kuma shirye-shiryen tunkarar duk wata annoba.

KARANTA WANNAN LABARIN: Malami SAN ya nesanta kansa daga binciken gidan Mai Shari’a Mary Odili
Ta rubuta kamar “ina jindaɗi na haɗuwa ta da Shugaba Biden a taron G20. Ina godiya akan goyon baya akan shirin rigakafi da shiryawa duk wata annoba. Ina matuƙar godiya da samun shawarwari daga manyan jami’ai na G20
Ga hotunan kamar haka: