Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari yayi taro da shuwagabannin tsaro a ranar Alhamis, domin ya karɓi jawabai akan yanayin tsaron ƙasar.
Mai ba Shugaban Ƙasa Shawara na Musamman akan Kafafen Yaɗa Labaru Femi Adesina ya bayyana haka a shafinsa ta Facebook.
Adesina ya tura hotunan taron, wanda Mataimakin Shugaba ƙasa Yemi Osinbajo da Manyan Hafsoshin Tsaron Ƙasar suka halar ta.
KARANTA WANNAN LABARIN: Ƴan ta’adda sun sanya bama-bamai, sun buɗe wuta a jirgin ɗaya ɗauko ni daga Kaduna zuwa Abuja — inji Shehu Sani
Mai ba Shugaban Ƙasar Shawara ya rubuta “Shugaba Buhari ya karɓi rahoton tsaro daga Hafsoshin Tsaron Nigeria a Villa, a ranar 21 ga watan Oktoba na Shekarar 2021.
Ga Hotunan Kamar Haka: