Shugaban Majalisar Dattijai Ahmad Lawan ya Isa Jahar Ekiti, inda za’a nada shi a matsayin Aare Akorewolu na Masarautar Iyin.
Wannan na kunshe ne a cikin wani jawabi da shafin Facebook na Shugaban Majalisar ya fitar, inda aka tura hotunan isar sa a Jahar.
Sanarwar tace, ” Shugaban Majalisar Dattijai Ahmad Lawan ya isa Filin Jirgi na Akure, Jahar Ondo, inda ya ke kan hanya zuwa Iyin-Ekiti na Jahar Ekiti, a yayinda za’a nada shi sarauta, Wanda Oluyin Iyin Oba Adeola Adeniyi Ajakaiye zaiyi.
KARANTA WANNAN LABARIN: Bama-Bamai: Mutum biyu sun mutu, 21 sun jikkata yayin da aka farmaki Motar Taliban
“Lawan, wanda ya isa Akure tare da rakiyar wasu Sanatoci, ya isa Filin Jirgin, inda ya samu tarbar wasu Sanatoci wanda zasu halarci taron.
“A lokacin taron, Lawan da kanshi za’a nada shi a matsayin Aare Akorewolu na Masarautar Iyin.