Cikin Kwana 2, Za A Iya Kamo Ƴan Boko Haram Da Suka Tsere — Ali Ndume.
Sanata Mai wakiltar Borno ta kudu, Ali Ndume, ya bayyana cewa, za’a iya kara kama yan Boko Haram din da suka gudu daga gidan gyaran hali na kuje cikin kwanaki biyu.
Dan Majalisar Dattawan ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis din da ta gabata a a yayin da ya bayyana a cikin Shirin siyasarmu a yau, wato Politics Today a gidan talabijin na channels TV.
KARANTA WANNAN LABARIN: Matsalar Tsaro: Kayi Koyi da Boris Johnson ka sauka daga Mulki — Ƴan Najeriya ga Buhari
A cewar sa, idan za’a baiwa dukkan Jami’an tsaro abinda suke bukata, zasu iya maido dasu.
” Idan dukkanin hukumonin tsaro zasu bai wa shuwaganni Jami’ai umarnin cewa su gano su cikin kwanaki biyu, zasu iya maido dasu.
“Ku tuna abinda Babangida yayi a wurin wani taro a lokacin da Anini ya tsare ya ci gaba da fashi ko ta ina yana kuma bannatar da kudaden gwamnati.
” A lokacin Babangida ya tambayi Inyang “Ina Anini yake? Bayan kwanaki biyu zuwa uku, sai ga Anini an samu nasar kamoshi.
” Kwanaki 100 kenan da yan ta’adda suka kai hari a hanyar jirgin kasa ta Kaduna zuwa Abuja, kuma har yanzu ba’a kamo su ba, yanzu kwanaki biyu da balle gidan gyaran hali ,kuma babu wanda zai ce ga inda mutanen suke. In ji Sanatan.
Idan ba a manta ba, a ranar talata ministan tsaro, Bashir Magashi, ya sanar da cewa, an rasa yan Boko Haram dake gidan gyaran hali na kuje .
Wasu yan bindiga a ranar talatar sun kai hari da bam a gidan kason.
Magashi ya bayyana cewa, Maharan yan Boko Haram ne, sannan fursunoni guda 64 da suka kasance membobin Boko Haram ne sun tsere ba a san inda su ke ba.