Jaridar Daily Trust ta labarto cewa cikin kwanaki uku kacal rahotanni sun tabbatar a tsakanin ranar Juma’a da Asabar a makabarta guda uku dake cikin garin Kano, an bizne sama da gawarwaki da suka rasu.
Wasu dai na fargabar ko cutar Koronabairos ce ta kashe su. Sai dai har yanzu babu wani gamsasshen dalili dake nuna cewa cutar ne ta kashe su.
Amma Ma’aikatar lafiya ta jihar Kano, sun tabbatar da cewa za su yi bincike domin tabbatar ko mene ne sanadiyyar wadannan rashe-rashe da ake yi.
Masu haka kaburburan sun ce adadin mutanen da suka rasu a ‘yan kwanakin wadanda suka yi aikin haka kaburburansu ba abu ne da suka saba gani ba kafin barkewar annobar korona.
Sai dai wadannan adadin ba su daga cikin adadin wadanda aka bizne a sauran kananan hukumomi takwas na cikin birnin Kano, inda masu haka kaburburan a sauran makabartu suka ce ba su ga wani sabon yanayi na daban kan mutuwar da aka yi ba a yankinsu.