A cikin kwana bakwai kacal an kama masu zama a Saudiyya ba a bisa ka’ida ba har su 15, 693 a yankuna da dama na kasar.
An kama mutanen ne a yayin wani kamfe na hadin guiwa da jami’an tsaro da hukumar da ke kula da fasfo (Jawazat) na kasar wanda suka gudanar daga 16 zuwa 22 ga Satumba.
Wadanda aka kama sun hada da wasu da aka kama suna kokarin tsallaka iyaka su shiga kasar, mafi yawansu ‘yan Yemen da wasu ‘yan Habasha.
Ma’aikatar harkokin cikin gida ta yi gargadin cewa duk wanda aka kama yana yi wa wani hanyar shiga kasar ba a bisa ka’ida ba na iya fuskantar dauri shekara 15 a gidan yari ko a ci shi tarar Riyal miliyan 1.