Kwalejin Ilimi ta Shehu Shagari (SSCOE) dake Sakkwato ta yaye dalibai 11,348 daga shekarar 2014 zuwa 2019.
Dr Muhammad Hakimi, shugaban Kwalejin ne ya bayyanawa manema labarai hakan a ranar Asabar, a wani mataki na shirya taron yaye daliban karo na 22 da kuma bukin cika shekara 50 da kafa makarantar.
Taron zai gudana ne a ranar Litinin 28 ga watan Disambar 2020.